7 Nuwamba 2016 - 15:28
Sudan Ta Samu Ci Gaban A Fuskar Karfin Soji

Shugaban Sudan ya sanar da cewa kasarsa ta samu gagarumin nasara da ci gaba a fuskar karfin soji ta hanyar gudanar da kere-keren makaman kare kai.

A jawabin da ya gabatar a yayin bikin girmama wasu tsoffin sojojin Sudan ta suka yi ritaya daga aikin soji a birnin Khartum a yau Litinin: Shugaban kasar Umar Hasan Albashir ya yi furuci da cewa: Sudan ta yi nasarar kera manya-manyan makamai da nufin kare kanta daga duk wani harin wuce gona da iri, kuma ta kai ga matsayin dogaro da kai a fuskar samar da irin makaman da take bukata.

Har ila yau shugaban kasar ta Sudan ya fayyace cewa: Rundunar sojin Sudan ta samar da wata sabuwar masana'antar kere-keren makamai irin na zamani, inda a ciki ake kera duk wani nau'in makaman da kasar ke bukata da nufin kare kasar.

Umar Hasan Albashir ya kuma kara da cewa: Gwamnatinsa ta fi bada muhimmanci ga batun tsaron kasa a duk kasafin kudin da take yi a kowace shekara, don haka ta yi nasarar kubuta daga makirce-makircen da ake kullawa kanta sabanin wasu kasashen da suke makobtaka da Sudan da makircin kasashen waje gami da matsalar 'yan tawaye suka yi awungaba da gwamnatocinsu.288